Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Shugaba Muhammadu Buhari ya Amince A Baiwa Cibiyar Yaki Da Cututtuka Da Ake Daukar Su Ta kasa Naira Miliyan Dubu 10.

buhari signs
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin gaggauta baiwa cibiyar yaki da  bazuwar cututtuka ta kasa naira miliyan dubu goma da tabukata domin samar da ingantattun kayakin aiki a dakunan ta na gwaje gwajen jirgin ruwa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafofi yada labarai Mal. Garba Shehu shi ya bayyana haka a cikin sanarwa da ya bayar a Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana cewa bada kudaden zai taimaka wa hukumar wajen magance kalubalen da take fuskanta wajen yaki da cutar coronavirus a kasar nan.

Yace shugaban kasar ya kuma bayar da umurnin kwaso wasu manyan ma’aikatan cibiyar guda 3 wadanda suka makale a Brazzaville babban birnin  jamhuriyar Congoinda suka halarci shirin bada horo wanda hukumar lafiya ta duniya ta shirya.

Yace daukan wadan nan matakai kari ne a kan sanarwar da hukumar yaki da cutar ta fadar shugaban kasa ta bayar da suka hada da rufe kan iyakoki na tudu da hana zirga zirgan jama’a na tsawon mako hudu da mayar da dukkan sansanonin alhazai cibiyoyin killace wadanda suke dauke da cutar ta COVID 19.

Sauran matakan sun hada da umurtan dukkan ma’aikatan gwamnati da ayyukan su bana musamman bane gudanar da ayyukan su daga gida.

Leave a Reply