Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja ya tafi kasar Amurka a yau don halartar taron majalisar dinkinkin duniya karo na 76 wato (UNGA76).
An bude taron a ranar Talata 14 ga watan Satumba.
Mr. Femi Adesina, mai magana ya yawun shugaban kasar ne ya bayyana hakan a rahoton da ya fitar ranar asabar a Abuja.
Taken taron na shekarar nan shine kafawa da jajircewa ta hanyar kwarin gwiwa sakamakon annobar COVID-19, da sake gina abubuwa da yadda za’a tunkare su dama mutunta hakkin jama’a da sake farfado da majalisar dinkin duniya.
Adesina ya bayyana cewa shugaban na Najeriya zai gabatar da jawabi a yayin taron a ranar Juma’a 24 ga watan Satumba inda zai yi magana kan da taro da abubuwan da suka shafi duniya baki daya.
Haka nan yace shugaban na Najeriya da tawagar sa zasu halarci taruka masu amfani harda bikin shekaru 20 na tunawa da Durban Declaration and Programme of Action wanda aka yiwa taken “yadda za’a gyara dokokin , wariyar launin fata da dai-daito kan mutanen Afrika.
San nan tawagar zata halarci taron harkar abinci, kan harkar makamashi, da kuma ranar dakile amfanin makamin Nuclear.
Acewarsa shugaba Buhari zai kuma gana da wasu shugabanni na duniya kan habbaka kungiyoyin duniya.
San nan Shugaban zai samu rakiyar Ministan kasashen waje Geoffrey Onyeama; Minisan shari’a na kasa Abubakar Malami da karamin Ministan muhalli Sharon Ikeazor.
Sai wadan da ke tawagarda suka hada da mai bawa shuugaban kasa shawar kan harkartsaro Maj-Gen. Babagana Monguno, Darakta Janaral na harkar tsaron sirri, Amb. Ahmed Rufai Abubakar; shugaban hukumar kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa da kuma Mataimakiyar shugaban kasar na musamman kan habbaka rayuwar jama’a, Mrs. Adejoke Orelope-Adefulire.
Haka nan Shugaban zai dawo kasar ranar 26 ga watan Satumba