Shugaba Buhari Ya Taya Shugabar Kasar Tanzania Mace Ta Farko Da Zata mulki kasar

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya sabuwar zababbiyar shugabar kasar Tanzanian Samia Suluhu Hassan wacce ta karbi shugabancin kasar bayan rasuwar marigayin shugaban kasar John Magufuli.

Hakan yana kunshe a cikin sanarwa da mashawarcin shugaban kasa na musamman MallamGarba Shehu a fitar a jiya 19 ga watan maris 2021.

Cikin sakon taya murna da shugaba Buhari ya aike mata, ya shawarci sabuwar shugabar kasar Suluhu, data hada kan kasar kuma ta jagoranci kasar bisa kyakkyawar kibla.

Shugaba Buhari ya kuma nuna aniyar hada kai da sabuwar shugabar cikin muradun Afirka dama na duniya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *