Shugaba Buhari ya nufi kasar Habasha domin halartar taron kungiyar tarayyar Afrika.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Rakiya Garba Karaye, Maiduguri
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis zai yi tattaki ta kwanaki hudu zuwa babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa, domin halartar taron shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka karo na 35.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimakawa kan harkokin yada labarai ta fadar shugaban kasa Femi Adisena, ya nuna cewa, shugaba Buhari zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka wajen nemo hanyoyin magance kalubalen siyasa, tattalin arziki da zamantakewar nahiyar mai taken “Building Resilience in Nutrition and Food Security on the African Continental.

Ƙarfafa Noma, Haɓaka Jarin Dan Adam, Ci gaban Al’umma da Tattalin Arziki.
A gefen taron na Tarayyar Afrika, shugaba Buhari zai gana da wasu shugabannin kasashen biyu, tare da nuna sha’awar inganta huldar kasuwanci, da hada kai don tinkarar kalubalen tsaro, da kulla alaka da cibiyoyi da dama domin samun ci gaba mai dorewa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Shugaban kasar zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ministan noma, Mohammed Abubakar da ministar harkokin bada agaji da walwalar jama’a Sadiya Umar Farouk.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, manjo janar Babagana Monguno da darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar, kuma zai bi sahun shugaban kasar a taron Tarayyar Afirka.

Leave a Reply