Shugaba Buhari Ya Kafa Kwamiti Kan Gyaran Sashin Kiwon Lafiya

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa wani kwamitin gyara sashin kiwon lafiya don fara ci gaba da aiwatar da shirin don yin gyare-gyare a fannin kiwon lafiya ga Najeriya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihohi da gwamnatin tarayya.

Wannan wani ci gaba ne day a biyo bayan rahoton binciken da Sashin kiwon Lafiya ya gudanar na hadin gwiwa tsakanin kamfanin Vesta da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.

Kwamitin zai gudanar da bitar dukkan sauye -sauyen kiwon lafiya da aka karba cikin shekaru ashirin da suka gabata da darussan da aka koya tare da sanya su cikin ci gaban sabon Shirin Sake gyarawa ayyukan na kiwon Lafiya.

Kwamitin wanda aka kafa na tsawon watanni shida karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya samu mambobi daga kwararrun masu kula da harkokin kiwon lafiya masu zaman kansu da na gwamnati, abokan hadin gwiwa na ci gaba, wakilai daga majalisar kasa da kuma kungiyar gwamnonin Najeriya da sauransu.

Abokan hulɗar kiwon lafiya na Vesta da gidauniyar Bill da Melinda Gates za su yi aiki a matsayin masu masu sa ido a cikin kwamitin.

A halin da ake ciki, Shugaba Buhari ya kuma amince da nadin Dr Ifedayo Morayo Adetifa a matsayin sabon Darakta Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC).

Shugaban ya bayyana shi a matsayin memba na wannan muhimmin kwamiti.

Leave a Reply