Shugaba Buhari Ya Jajantawa jamhuriyyar Niger Bisa Kisan Gilla Da Aka Kai Yankin Tillaberi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ala wadai bisa farmaki da aka kaiwa ayarin motoci dake hanyarsu ta dawowa a kasuwar mako a yankin Tillaberi na jamhuriyyar Nijar wanda jama’a da dama suka rasa rayukan su, sannan shugaba Buhari ya mika ta’aziyar sa ga iyalan mamatan baki daya dama kasashen dake makwabtaka da Najeriyan.

Shugaba Buhari yayi ala wadai da harin kuma yace Najeriya zata kasance da makwabtan ta a yakar ta’addanci da akeyi.

Hakan yana kunshe cikin sanarwa da mashawarcin shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya fitar ranar 17 ga watan maris 2021.

Shugaba Buhari yace kashe-kashen ya bayyana irin matsalar tsaro dake fuskantar jamhuriyyar Niger gab lokaci da kasar ke shiryen-shiryen nada sabon shugaban kasar su Mohamed Bazoum tare da cewa dole sai yankin sun hade domin kawo karshen yan ta’adda.

Mayakan sun tare jerin ayarin motoci ne a kudu maso yammacin a Nijar a hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako sannan suka kai hari wani kauye a yankin Tillaberi dake kusa da iyakar Mali da Burkina Faso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *