Shugaba Buhari Ya Bayyana Jin Dadinsa Na Cigaban Da Aka Samu Tsakanin Najeriya Da Norway

BUHARI FEC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadinsa na cigaban da aka samu na alakar dake tsakanin Nigeria da Norway cikin shekaru 4.

Mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkar labarai da hulda da jama’a Malam Garba Shehu.

Ya bayyana cewa shugaban kasar ya bayyana hakan a ganawar sad a jakadan kasar ta Norway da Nigeria Jens-Petter Kjemprud.

Buhari ya yabawa jakadan kan kokarin da yayi tsakanin kasashen ta fannin man fetur da iskar gas, da kiwon kifi, bada agajimusammman a Arewa maso gabas.

A nashi jawabin jakadan yace shekarun nashi 4 sun habbaka tattalin arzikin kasashen 2 matuka.

Haka nan yace wajen kimanin kamfanonin Norway 70 suka zuba jari a Najeriya ta fannin chanji.

San nan ya bayyanna cewa yana ya taimaka ta inda wasu kungiyoyin bada agaji na Norway suka tara fiye dad ala biliyan daya don bada agaji a Arewa maso gabas.

Related stories

Leave a Reply