SERAP Ta Aikawa Shugaba Buhari Wasika Kan Batan Naira Biliyan 3.1 A Ma’aikatar Kudi

Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki ta (SERAP) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi amfani da kyawawan ofisoshin sa wajen umartar babban mai shari’a na tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami, SAN, da hukumomin da suka dace da yaki da cin hanci da rashawa da su binciki zargin cewa N3bn na kudaden al’umma sun bata, ba a sarrafa su ko kuma an karkatar dasu daga ma’aikatar kudi ta tarayya.

Kungiyar ta ce an tattara wadannan zarge-zargen ne a cikin rahotannin shekara-shekara na 2018 da 2019 da babban mai binciken kudi na tarayya ya tantance.

SERAP ta ce: “Duk wanda ake zargi da hannu a cikin lamarin to ya fuskanci hukunci kamar yadda ya dace, idan akwai isassun shaidun da za a iya amincewa da su, kuma duk wasu kudaden da suka bace ya kamata a kwato su gaba daya.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 24 ga Disamba, 2021, kuma mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce: “Rahotanni sun nuna babban cin zarafin jama’a ne. A matsayinta na mai kula da kudaden jama’a, ya kamata ma’aikatar kudi ta tabbatar da bin ka’idoji da tsare-tsare na gaskiya da rikon amana.

Wannan jagoranci yana da mahimmanci ga Ma’aikatar don jin daɗin amincewar jama’a don tasirinsa.

SERAP ta ce: “Zarge-zargen da ake yi cewa N3,143,718,976.47 na kudaden jama’a sun bace, zai kuma kasance a fili karara wanda ya zama wani babban karya dokokin yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kuma wajibcin yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kasa da suka hada da yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa wadda Najeriya ta kasance jiha.

“SERAP ta lura cewa sakamakon cin hanci da rashawa ya shafi ‘yan kasa ne a kullum. Kuma Cin hanci da rashawa yana jefa su cikin ƙarin tsadar rayuwa, kuma yana lalata ci gaban tattalin arzikin ƙasar, tare da jefa mafi yawan ƴan Najeriya cikin talauci da hana su ayyukan yi.

An kwafin wasikar zuwa ga Malami; Farfesa Bolaji Owasanoye, Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifukan (ICPC); Abdulrasheed Bawa, Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC); Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da t.sare-tsare ta kasa; da shugabannin kwamitocin asusun gwamnati na majalisar dokokin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *