Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Sarkin Swazi Ya Karyata Rahoton Cewa Ya Umarci Maza Su Auri Mata 5

swazi king
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil

Gwamnatin kasar swazi dake yankin Afrika ta kudu ta karyata rahoton da aka ce sarkinta Mswati na uku ya umarci maza da su auri mata fiye da hudu ko su fuskanci hukuncin shari’a.

Mai Magana da yawun gwamnatin ya bayyana cewa babu irin wannan dokar inda yace wasune suka kirkiro shi.

Labarin ya fito ne daga mai lura da al’amura na kasar Zambia inda wasu gidajen jarida da dama suka wallafa domin batawa sarkinsu suna.

Sarki Mswati na uku yasha samun irin wannan rahotanni da suke batashi a idon duniya inda jaridun kasasshen, kafafan sada zumunta, da wasu kungiyoyi suka sha wallafa wa.

Ya kara da cewa wannan kagen da akayi musu ba wai ya bata sarautar bane kawai harda al’adarsu da kuma aikin jarida baki daya.

Haka zalika ya bayyana cewa suna rokon yan jarida na kwarai da jama’a da su kaurace wa wadannan rahotanni marasa inganci.

Related stories

Leave a Reply