Sarkin Musulmi Yayi ‘kira Da Shuwagabanni Addinin Da Su Kasance Masu Fadin Gaskiya A Koda Yaushe .

Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, dake yankin Arewa maso yammcin Najeriya ya yi ‘kira ga limaman addinin kirista da su ci-gaba da yin wa’azi mai inganci da zai hada kawunan al’umma.

Basaraken ya bayyana hakanne a sa’ilin da yake ganawa da manya-manyan malaman Cocin katolika a ya yinda suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa dake birnin Sokoto.
Ya ce yana da kyau shuwagabanni su kasance masu fadin gaskiya a koda yaushe su kuma daina sajewa da sunan addini suna cutar da al’umma.

Haka zalika Sarki Sa’ad ya basu tabbacin cewa zai basu duk wata gudumuwa da ya kamata domin tabbatar da zaman lafiya a ‘kasar baki daya.

Ya ‘kara da cewa wannan ziyarar zai ci-gaba da haifar da fahimta tsakanin addinan biyu.
Shima a nasa 6angaren shugaban bishop-bishop na katolika Archbishop Augustine Akubueze, ya yabawa basaraken game da yunkurinsa na ya’kar ta’addanci a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *