Najeriya: Sarkin Gudi A Jihar Yobe Yayi Kira Ga Malamai Su Guji Wa’azin Da Zai Tada Rikici

By: Nuhammed Nur Ali

Sarkin Gudi da Gadaka na karamar hukumar Fika a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya Alhaji Isa Bunuwo Khahaja, ya kirayi malamai da su guji wa’azin da zai tada rigima da rabuwar kawuna a wannan watan na Ramadan.

Sarkin yayi gargadin ne yayin da yake ganawa da manema labarai a fadar sa dake garin Gadaka.
Haka nan ya kirayi malaman da su karkatar da wa’azin su wajen zaman lafiya da kyakykyawar mu’amala a tsakanin mutane.

Sarkin yace ya kamata a dinga karfafa zaman lafiya tsakanin al’umma wanda zai kawo zaman lafiya da hadin kan yan kasa a jihar Yobe State da kasa baki daya.

Haka nan ya kirayi masu hannu da shuni dasu taimaki wadanda basu da karfi da abinci, ko kudi don su samu suyi azumin cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *