Sanata Muhammad Abba Aji yayi rigister da kamfanin hadin kan iyaka da hukumar kula da harkokin kamfanoni.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sanata Muhammad Abba Aji ya kasance dan Najeriya na farko da ya yi rijistar kamfanin hadin kan iyaka da hukumar kula da harkokin kamfanoni.

Sanatan, wanda ya nuna farin cikin sa bayan ya karbi takardar shaidar rijista daga hukumar kula da harkokin kamfanoni ya ce zai yi amfani da damar yadda ya dace.

Ya ce yana alfahari da samun wannan nasara tun yana dan shekara 70 bayan da aka kira shi cikin lauyoyin Najeriya a matsayin lauya a shekarar da ta gabata yana da shekaru 69.

Ya nuna godiya ga magatakarda da kuma hukumar kula da harkokin kamfanoni saboda karramawar da suka yi masa na kasancewa na farko da aka yi rijista abokan hulɗa na iyakantacce.

Leave a Reply