Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Sanata Ibrahim Gaidam Ya Mayar Da martani kan Sukan Shirin Dokar Da Ya Gabatar Ga Abokan Aikinsa A Majalisar

Gov-Ibrahim-Gaidam
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Tsohon Gwamnan jihar Yobe kuma Sanata dake wakilar Yobe ta kudu a majalisar dokoki ta kasa, Sanata Ibrahim Gaaidam yace babu wani rarrashi da zai yiwa ko wane dan majaliya goyi bayan kudurin da ya gabatar na neman kafa dokar da zata bayar da damar samar da Hukuma ta kasa da zata kula da bayar da ilimi da koya sana’o’i ‘Yan tayar da kayar baya da suka tuba a kasar nan.

Sanata Ibrahim Gaidam wanda yake mayar da martani kan sukan shirin dokar da ya gabatar da abokan aikinsa a majalisar suka yi, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa shi idanunsa ba a rufe suke ba, kan lallai sai an amince da shirin dokar da ya gabatar ko ta halin kaka.
Yace shi bai tuntubi Shugaban majalisar dattawan ba, Sanata Ahmaad Lawan kafin ya gabatar da kudurin dokar, inda yace shi bai ga dalilin da zai sa ya tattauna da ko wane dan Majalisar ba akan shirin dokar.
Yace shirin dokar ba yana magana akan wadanda Sojoji suka kama ba ne, sai dai wadanda suka yi nadama sannan suka mika kansu da kansu.
Sanata Ibrahim Gaidam yana mayar da martani ne akan sukan shirin dokar da Tsohon shugaban masu rinjaye a majjalisar, Sanaata Ali Ndume yayi, inda yace sukan shirin dokar da Sanatan dake wakiltar Borno ta kudu ya yi, ta nuna a fili irin zargin da ake yi masa na cewa yana da dagantaka da ‘Yan kungiyar Boko Haram.

Leave a Reply