
A yanzu haka dai, sama da maniyata 13,000 ne suka isa birnin Madina, na kasar Saudiyya. Wata sanarwa daga hukumar jin dadin alhazai ta kasa ta bayyana cewa kawo yanzu, anyi jigilar alhazai sau 27.
Mahajjata wadanda suka hada daga jihohin Kano, Katsina da Lagos tuni suka isa birnin Makka daga Madina.
