
Sabuwar shugabar kungiyar tarayyar turai tace ta zabi kasar Afrika a matsayin kasar da zata fara ziyarta, sakamakon yadda kasar tacke cigaba da sauri ta fannin tattatlin arziki da kuma kalubalen da suke fuskanta ta fannin canjin yanayi.
Shugabar Ursula von der Leyenta bayyana hakan bayan ta gana da Prime Minista na kasar Ethiopia Abiy Ahmed a ofiishinsa Addis Ababa a kasar ta Ethiopia.
Kungiyar tarayyar turai ta bayyana cewa ta bada kudin Euro miliyan 170 don taimawa tattalin arzikin kasar Ethiopia da kuma zaben da zasu gudanar a watan Mayu.
Prime Minista Abiy Ahmed yace suna bukatar wasu kudaden saboda yadda suke da yakinin abubuwan da suka sa gaba.
Von der Leyenta kara da cewa tayi wata ganawar da hukumar kunyar tarayyar Afrika wanda Union Moussa Faki Mahamat ya jagoranta inda suka tattauna kan hijira, tsaro da kuma wasu matsalolin da ake fuskanta a yankin.
