Rundunar Yansandan Najeriya Sun Cafke Masu Garkuwa Da Yanfashi 93

Rundunar yan sandan Najeriya sun cafke mutane 93 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a babban titin Abuja zuwa kaduna.

An kamasu ne karkashin rundunar da aka kafa domin kawo karshen ta’addancin garkuwa da mutane da ma wasu manyan laifuka da ake yi akan titin.

An gabatar da wadanda ake zargin a garin katari ranar alhamis bayan kamasu da akayi a garuruwan Kachia, Lere, Igabi, Kagarko, Birnin Gwari, Zaria, Minna da wasu kauyukan dake kewayen.

An samu mugan makamai da dama daga wurinsu hade da kakin sojoji, jabun kudaden kasashen waje da motoci guda biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *