Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Rundunar Yansandan Jihar Adamawa Ta Kama Masu Garkuwa Da Yanfashi

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

From: Hamisu Ado Nguro, Damaturu
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, Aliyu Adamu Alhaji, ya fara kai farmaki kan masu satar mutane da ‘yan fashi a cikin jihar inda yasha alwashin tabbatar da cewa ayyukan aikata laifuka sun sun zama tarihi a jihar baki daya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun DSP Suleiman Yahaya Nguroje, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan .

A cikin sanarwar, rundunar ta ce a ranar 20 ga Maris, ta kama mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da Injiniya Elan Jobbo, shugaban makarantar VTC Jabbi Lamba, Alhaji Jauro Mamburso da Alkani Zumbe inda aka kama, dukkansu a kananan hukumomin Girei da Song cikin watan Mayu na shekarar 2020.

A cewar rundunar, wadanda ake zargin sun hada da Usman Sale dan shekara 40, mazaunin Muleng, karamar hukumar Song; Lawali Sale mai shekara 37, mazaunin Kauyen Bah Usman, da ke karamar Hukumar Fufore da Yerima Alhaji Dadi mai shekara 36, ​​wanda ke zaune a kauyen Bah Usman, da ke karamar Hukumar Fufore.
Rundunar ta kara da cewa an cafke su ne a maboyarsu da ke kauyukan Muleng da Chigari na kananan hukumomin Song da Fufore.

DSP Nguroje ya kara da cewa bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa wadanda ake zargin suna shiga cikin fashi da makami da ayyukan satar mutane a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Kamaru.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Aliyu Adamu Alhaji, ya yabawa DPO na Song da mutanensa saboda kokarin da suka yi

Leave a Reply