Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta kama wani dan kasar China Akan Lalata Kayakin Layin Dogo.

Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta kama wani dan kasar China da mai bada shawara na musamman ga gwamna Abdullahi Sule kan ayyuka da wasu mutane 15 kan zargin lalata kayakin layin dogo.

Kwamishinan yan sandan jihar Mr. Bola Longe shi bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Lafia.

Yace sauran wadanda ake zargi cikin barnar akwai jami’an yan sanda 2 masu mukamin sufeta da kuma sajent da suke sashen binciken masu laifi da kuma jami’in tsaron farin kaya na civil defence.

Kwamishinan yace an kama masu laifin a wajajen daban daban inda suke daukan kayakin layin dogo a ranakun 16 da 24 ga wannan wata a Agyaragun Tofa a Lafia da kuma Kadarko a karamar hukumar Keana na jihar.

Haka kuma an kama wani manajan kamfanin karfe a Tunga Maje dake birnin tarayya wanda ake zargin shine mai siyan kayakin.

Daga karshe kwamishinan yace ana udanar da bincike a sashen binciken masu laifi na jihar.