Rundunar Sojojin Saman Najeriya Sun Lalata Guraren Boko Haram A dajin Sambisa

Rundunar sojojin saman Najeriya karkashin Operation Lafiya Dole sun kashe yan ta’adda da dama hade da lalata gurarensu dake dajin Sambisa a Jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahoton ya fito daga daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin saman Air kwamanda Ibikunle Daramola ranar litinin a Abuja.

Yayin harin sun lalata yawancin guraren da yan ta’addan suke aiki dasu san nan sun kashe da dama daga cikin su ranar 10 ga watan Yuni bayan samun bayanan sirri.

Daramola ya kara da cewa sun gano wani guri cikin kauyen Alafa a yankin dajin Sambisa da yan ta’addan suke amfani dashi wajen gudanar da ayyukansu.

Jirgin da ya kai hari gurin inda ya samu nasarar tarwatsa guraren da yake so ciki harda yankin da suke gudanar da ayyukan su hade da kashe yan ta’addan Boko haram da dama.

Ya kara da cewa sojojin saman zasu hada kai dana kasan don kara tarwatsa yan ta’addan a arewa maso gabashin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *