Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Samu motar Tanki Na Yaki Daga Kasar China.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Hamisu Ado Nguru
Rundunar sojojin kasar Najeriya ta samun kayakin aiki da suka hada da tankar VT 4 daga kasar China a kokarin ta na karfafa ayyukan tsaron sojojin kasa wajen yaki da yan kungiyar Boko Haram.

Kayakin wanda aka yi odar su daga kasar China tun ranar 8 ga watan Maris akan dala miliyan dari 1 da 52.

Shugaban tsare tsare na rundunar sojojin kasa laftanar janar Lamidi Adeosun yace kafin a samu kayakin ya dau lokaci amma yanzu sun godewa Allah da kayakin suka iso.

Ya kara dacewa gwamnatin tarayya tana kokari ba ta fannin samar da kayaki ba har ma da yadda za’a magance matsalar tsaro a kasar.

Ya kara dacewa kayakin sun hada da tankin ruwa da tankin ruwan zafi da motar yaki da na’urar daukar hoto kuma an horar da wadan da zasu sarrafa kayakin.

A watan Mayu na shekara 2019 ministan tsaro birgediya janar Mansur Dan Ali yace gwamnatin Najeriya ta ware da kudade domin samar da kayakin zamani ga rundunar sojojin Najeriya.

Leave a Reply