Rundunar Sojojin Najeriya Ta Bayyana Kisan Jami’anta A Jakana Dake Jihar Borno

army-logo
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojojin Najeriya sun tabbatar da rasuwar Kanal, kaftin, da wasu sojoji 3 da ‘yan kungiyar Boko Haram sukayi a jihar Borno.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar Operation LAFIYA DOLE, Kanal Isa Ado ne ya bayyana hakan a Abuja.

Inda yace abun ya faru ranar Laraba a garin Jakana dake jihar Borno bayan da jami’an suka tsaya a hanyar su ta Maiduguri zuwa Damaturu wanda hakan yasa ‘yan ta’addan sukayi musu kwantan bauna.

Ado ya kara da cewa jami’an dake bataliya ta 212 dake aiki a yankin na Jakana sun bawa ‘yan ta’addan kashi inda suka kashe da dama.
Haka nan ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sunzo da misalign karfe 6:45 na yamma a motoci masu dauke da bindigogi guda 7 inda suka so su shiga sansanin basu samu dama ba inda jami’an yi musayar wuta da jami’an.

Related stories

Leave a Reply