Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Rundunar Sojojin Najeriya Sun Kore Mayakan ISWAP A Damasak

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A ranar alhamis ne rundunar sojojin Najeriya suka fatattaki yan ta’addan ISWAP karo na biyu da mayakan ke sake kai farmaki kwanaki kadan da suka kai hari yankin Damasak na jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Garin Damasak dake iyakar jamhuriyyar Niger da Kamaru nada kilomita 180 da birnin Maiduguri.

An ruwaito cewa yan ta’addan sun kona,motocin jin kai guda 2 kuma suka tafi da guda daya.

Yan ta’addan sun kai farmakin a karamin hukumar Mobbar a tsakanin yammacin lahadi da kuma safiyar litinin.

A janairun 2019 daya gabata, rundunar sojin saman Najeriya ta rasa jirgin ta bayan ta kurmushe yayin kai agaji ga bataliya na 145 a garin na Damasak.

Haka zalika a watan yuli na shekarar, yan ta’addan sun hari jirgin agaji wanda jirgin ya samu dawowa birnin Maiduguri.

Leave a Reply