
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana ranar litinin cewa ta kashe 9 daga cikin ‘yan ta’addan ISWAP da suke musu aiki a kafafen sadarwa na zamani.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar kanal Sagir Musa ne ya bayyana hakan a rahoton daya fitar, inda yace jami’ansu sun musu illar da baza su sake samun damar samun yancin ayyukan su ba.
Sunayen da suke amfani da kafafen sadarwar sune Abu Hurayra al-Barnawi, Ali al-Ghalam al-Kajiri, Abu Musab Muhammed Mustafa al-Maiduguri, Abu Abdullah Ali al-Barnawi, da Abu Musa al-Camerooni.
Ragowar sune Ahmed al-Muhajir, Abu Ali al-Bamawi, Abu Khubayb bin Ahmed al-Barnawi, Abu al-Qa’qa’ al-Maiduguri.
Ya kara da cewa wadan nan kungiyar sun dade suna yada karya a kafafen sadarwa na zamani.
Gidan Radiyon Dandal Kura ya lura cewa Boko Haram suna amfani da kafafen tun shekarar 2009, inda suke samun sababbin mayaka daga Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru.
