Rundunar Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Boko Haram da dama A Jihar Borno

rundunar sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole sun kashe yan kungiyar Boko Haram da dama a karamarr hukumar Mobbar dake arewacin jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Jami’in mai hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya birgediya janar Texas Chukwu, shi ne ya tabbatar da hakan.

Ya cigaba da cewa mayakan sunyi niyar kai hari kan sojojin su amma hakkarsu bata cimma ruwa ba, domin kuwa sojin sun tarwatsa motocinsu tare da kashe galibinsu.

Cikin abubuwanda sojin suka samu daga hannun mayakan akwai bindiga kirar AK47 guda hudu, da motoci biyu, da kuma alburusai masu yawan gaske.

Haka zalika ya kara da cewe ya yin musanyar wutar jami’an soji guda bakwai sun jikkata, sa’annan wasu daga cikin mayakan sun tsere ya yin artabun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *