
By: Yabawa Ismaila Borno
Rundunar sojojin Najeriya na Operation Lafiya Dole da hadin gwiwar yan kungiyar sa kai sun lalalata matsugunin yan kungiyar Boko Haram dake kauyukan Ma’allasuwa da Yaga – Munye ranar Laraba a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.
A rahoton da mai Magana da yawun rundunar ya fitar Kanal Sagir Musa ranar litinin ya bayyana cewa jami’an nasu basuyi gaba da gaba da mayakan ba sun tsere kafin zuwan jami’an tsaron inda suka gudu suka bar mutanen da sukayi garkuwa dasu 54 wanda 29 daga ciki tsofaffin mata ne sai yara maza da mata 25.
Ya kara da cewa a kauyukan Zari – Kasake da Jumachere dake Damasak a karamar hukumar Mobbar a jihar Borno jami’an dake Bataliya 145 sun samu wasu motocin aikin Boko Haram guda biyu yayin da suke kakkabe yankin.
Haka nan sun kama wani dansandan Mopol mai suna Sergeant Markus John a gurin bincike na Njimtilo dake hanyar Maiduguri zuwa Damaturu da bindigogin magazines guda 2 da harsashai 146 da kuma wata bindigar mai harbor jirgin sama boye a cikin jakarshi a hanyarshi ta zuwa jihar Legas.
Haka zalika ranar 10 ga watan Mayu na shekarar 2019 jami’an Operation Lafiya Dole da hadin gwiwar jami’an yansanda sun kama wasu masu suna Paul Ojochegbe da kofural Oko Eke da bindigar AK 47 da ba’a hada ba a gurin bincike na N’jimtilo.
