
By: Babagana Bukar Wakil Ngala
Rundunar sojojin Najeriya na operation HARD STRIKE da hadin gwiwar yan kungiyar sa kai na civilian JTF sun gudanar da ayyukan kakkabe dajikan dake yankin kauyukan Fuye da melere a jihar Borno dake arewa maso gabshin Najeriya.
Rahoton ya fito daga kanal Sagir Musa daraktan hulda da jama’a na rundunar, inda yace rundunar sojin da hadin gwiwar yan kungiyar yan sa kai din sun fafata da mayakan na Boko Haram a garin Gulwa inda jami’an suka kashe yan ta’addan 7 suka samu harsasai da dama.
Ba’a samu rauni ba ta bangaren jami’an sojin da yan kungiyar sa kan, haka nan ya jaddada kokarin rundunar na ganin an kawo karshe yan ta’addan na Boko Haram.
Rundunar tace zata ci gaba da wayarwa mutane kai, haka nan zata samar da lambobin waya da za’a kira a dinga bada rahotanni ga jami’an tsaro a kasa baki daya.
