Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Rundunar Sojoji Sun Kashe Yan Kungiyar Boko Haram 41 Tare Da Ceto Wasu Mutane 60 Gamboru.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojojin Najeriya karkashin shirin operation lafiya dole sun kashe yan kungiyar Boko Haram dana ISWAP sama da 41 yayin gwabzawan da sukayi a Gulwa da Musuni a karamar hukumar Ngala na jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar birgediya janar Muhammad Yerima shi ya bayyana haka a wata sanarwa, yace an samu nasarar ne a ranar Litinin.

Yace an ceto wasu mutane sama da 60 daga hannun yan ta’addan tare da kwato makamai da dama yayin fafatawar su.
Rundunar sojojin sun fafata da mayakan na kusan mintuna 45 wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutuwar 41 daga cikin yan ta’addan.

Kayakin da aka kwato daga hannun yan ta’addan sun hada da bindigogin AK 47 12, babur, kekuna 6, kaken dinky da abubuwan na hada abin fashewa.
Hafsan sojojin saman ya yabawa rundunar bisa kokarin su.

Leave a Reply