Rundunar Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Yan Bindiga 12 A Kaduna

Nig-Airforce-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Operation Diran Mikiya na karkashin rundunar sojin saman Najeriya da hadin gwiwar Karin jami’an su na yanki na 271 sun kashe yan bindiga 12 a dajin Kamuku dake Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Sun bayyana cewa yayin harin sun ceto mutuum 15 da akayi garkuwa dasu a dajin a ta bakin jami’in hulda da jama’a ba rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola yayin da yake bayanin ranar Talata a Abuja,

Ya kara da cewa a kwanan nan NAF suka kaddamar da jami’an da suka kara a Birnin Gwari dake jihar Kaduna don kawo karshen ta’addanci a kasa baki daya.

Haka nan ya bayyana cewa sun kai harin ne ta hanyar bayanan sirri da suka samu inda aka bayyana musu cewa suna dajin Kamuku dake Tsakanin karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna da karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Harin ne yasa yan bindigar suka guda wadanda akayi garkuwa dasu suka samu suka gudu zuwa kauyukan dae kusa. Haka nan jami’an sunce zasu cigaba da hada karfi da ragowar jami’an tsaro.

Related stories

Leave a Reply