Rundunar Sojin Najeriya Ta Binne Jami’anta 5 A Barikin Maimalari Dake Maiduguri

army-logo
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin Najeriya tace bazata yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kawo karshen rikicin ta’addancin Boko Haram a Arewa maso gabas.

Sabon gwamandan mayakan Operation Lafiya Dole Maj-Gen. Olusegun Adeniyi ne ya bayyana hakan ya bayana hakan yayin bikin binne gawar jami’ansu 5 da suka rasu a makabartar sojoji ta cikin barikin, Maimalari a Maiduguri.

Adeniyi ya kara da cewa jami’an baza su gaji ba har sai an kawo karshensu da samun zaman lafiya a yankin baki daya.
Haka nan ya bayyana wadanda suka rasun a matsayin jarumai wadanda suka sai da rayuwarsu wajen kare kasar su.

Maj-Gen. Olusegun Adeniyi ya bayyana abun da ya faru a matsayin abin bakin ciki kuma yan tunasar da iyalansu cewa wan nan sojojin sun sadukar da rayuwarsu wajen kare kasar su ta haihuwa.

Adeniyi ya bayyana sunayen sojijin da suka rasu kamar haka Col. Kenneth Elemele, Lance Corporals Ajijola Sunday, Oguntuase Ayo, Dimos Danial da Private Akinola Ayoola.

Related stories

Leave a Reply