Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Rundunar Sojin Najeriya Sun Karyata Faifan Boko Haram Kan Batan Jirginsu Da Ya Bata

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An kirayi hankalin rundunar Sojan Sama ta Najeriya kan wani bidiyon da ake yadawa a kafafen sada zumunta, da kafofin yada labarai inda ake zargin cewa jirgin rundunar na Alpha Jet, wanda ya bata a jihar Borno ranar 31 ga Maris 2021 mayakan na Boko Haram ne suka harbo shi.

Rundunar tace wan nan bidiyoyin, ya fara ne da harbe-harbe daga wasu ‘yan ta’adda, ciki har da yara kanana kan babura da ababen hawa.

Daga baya aka tsallake kwatsam zuwa wurin da ke nuna wani jirgin saman ne yake fashewa a tsakiyar iska, sakamakon harbin da akayi masa.

Rundunar tace wani bangare na bidiyon ya nuna wani dan ta’adda, wanda, yake tsaye kusa da kayan jirgin da suka tarwatse yana ikirarin cewa sun harbo jirgin na NAF din ne.

Sunce har yanzu ana kan nazarin bidiyon sosai, inda kowa ya gani yawancin sassan bidiyon an shirya su ne da gangan ba don da gaske su suka harbo jirgin ba.

Haka nan shirin bidiyon ya kasa nuna takamaimai yadda abun ya fara har aka kai ga yadda jirgin ya fadi kasa.
Rundunar ta kuma bayyana cewa, kusan abu ne mai wuya jirgin sama ya fashe a tsakiyar iska, kamar yadda aka nuna a bidiyon, kuma har yanzu yana da bangare mai kyau na burbushinsa, gami da wutsiyarsa.

Haka nan sunce kungiyar ta Boko Haram, na da ɗabi’ar amfani da farfaganda na ƙarya, don neman suna wanda daga gani wasu dalilai suka haifar da hakan.

Sakamakon haka, ana shawartar ‘yan Nijeriya da su yi watsi da abubuwan da ke cikin bidiyon da ke zagayawa har sai an kammala dukkan bincike kan yadda jirgin ya fadi.

Haka nan a nata bangaren rundunar na aiki tukuru don ganin ta hada kai da sauran hukumomin don kawar yan ta’adda daga yankin Arewa maso Gabas.

Leave a Reply