Ramadan: Shugaban Kasar Najeriya Ya Kirayi Mutane Dasu Zauna Lafiya

By: Hasan Ali Marte

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kirayi yan kasar da su ci gaba da zama lafiya da junansu yayin da Musulmai suka fara azumin Ramadan ranar litinin.

Wan nan sakon na Buhari ya fitar dashi ne ranar Lahadi da daddare bayan an bayyana ganin watan na Ramadan.

Shugaban yace addinin na musulinci addini ne da yake na zaman lafiya da mutunta juna wanda yake hani da tsana da kuma tashin hankali.

Haka nan ya kirayi Musulmai dasu zauna lafiya da junansu da ragowar wadanda ba musulmai ba.
Shugaba Buhari yayi addua kan Allah ya cigaba da bawa Najeriya zaman lafiya cigaba da kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *