Prime Ministan Kasar Mali Da Ma’aikatansa Sun Sauka Daga Aiki

Prime Ministan kasar Mali da ma’aikatansa gaba daya sun sauka daga aiki bayan da aka samu hargitsi a kasar inda aka zargi Soumeylou Boubeye Maiga da rashin daukar mataki har aka kashe makiyaya da dama daga yan hamayyarsu.

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya bayyana cewa ya karbi barin aikin da Mr Maiga da ministocin shi suka yi, kuma za’a bayyana sunan sabon Prime ministan bada dadewa ba inda za’a kafa sabuwar gwamnati da duk yan siyasar su.

Mali ta dade tana fama da rikici tunda yan tsatstsauran ra’ayin Islama na Al-Qaeda suka biyo ta arewacin saharar kasar a shekarar 2012.

Duk da jami’an soji dake yankin da kuma yarjejeniyar da aka gudanar a shekarar 2015 mujahidan na rike da manyan gurare a kasar.

Haka nan gwamnatin kasar ta samu matsin lamba kan kasa dawo da kwanciyar hankali kasar musamman bayan kisan Fulani makiyaya 160 a yankin Mopti.

Yan ta’adda da makamai da bindogi daga kabilar Dogon ne suka kaiwa Fulani makiyaya hari. Kasar dai ta girgiza da kisan dubban mutane, wanda hakan yasa suka fito babban titin birnin kasar ta Bamako ranar 5 ga watan Aprilu don zanga-zangar rashin jin dadin abinda ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *