Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Ogunlade Ya Zama Sabon Shugaban Rundunar Hadin Gwiwa Ta MNJTF

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Manjo Janar Jide Ogunlade ya karbi matsayin kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Forcewato (MNJTF), bayan nadin da aka yi masa kwanan nan.

Ogunlade ya karbi jagorancin rundunar ne daga Manjo Janar IM Yusuf wanda aka nada a matsayin Shugaban Ayyuka na Hedikwatar Sojojin ta Najeriya.

A cewar wata sanarwa da aka sanya wa hannu, Kanar Muhammad Dole, Babban Jami’in yada labarai na Sojojin MNJTF a Ndjamena,yace an fara gudanar da hanyoyin mikawa da karbanmukamin ne a ranar Juma’a 12 ga Maris inda akayi biki a hukumance ranar 19 ga watan Maris na shekarar nan.

Acewar rahoton bikin ya samu halartar wakilai daga kungiyar kashen turai, kungiyoyin majlisar dinkin duniya, kungiyar kasashen Afrika, cibiyar tsare-tsare da manema labarai.

Yayin da yake jawabi Yusuf ya yabawa jami’an dake Hedikwatar da kokarin da sukeyi inda ya bukace su su marawa wanda ya gajeshi baya.

A nashi bangaren sabon kwamandan ya godewa tsohon shugaban da hadin kan day a bashi da dukkanin abokan aikinsu.

Haka nan ya tabbatar wad a jami’an rundunar cewa kullum a shirye yake yaga an sasanta har sai an kawo karshen ta’addanci.

Leave a Reply