
‘Yan najeriya naci gaba da kushe yadda ayyukan ta’addanci suke karuwa a kasar, hukumar wayar da kan yan kasa wato NOA ta kirayi yan Najeriya dasu bar jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu kan ‘yan bindiga da ‘yan fashi basu dinga maida abun siyasa ba.
Darakata Janaral na hukumar Dr. Garba Abari ne yayi wan nan kiran bayan kisan Mrs. Funke Olakunrin, yar shugaban Afenifere Pa Reuben Fasoranti.
Yayin da yake wa iyalan marigayiyar ta’aziyya Darakta Janaral din ya bayyana cewa ko wane dan najeriya nada rawar da zai taka wajen yaki da ta’addanci a kasar.
Abari ya kirayi yan siyasa dasu dena kiran sunan wasu suna danganta su da ayyukan ta’addanci wanda hakan zai raba kan kasar.
Haka nan Abari ya bayyana cewa ana kashe kashen a yankuna da yawa ne akasar wanda yake bukatar hadin kai da alla wadai ga duk wani dan Najeriya.
