NLC Ta Gargadi Gwamnatin Najeriya Kan Cire Tallafin Mai

Kungiyar kwadago ta kasar Najeriya wato NLC ta kirayi gwamnatin kasar kan kar ta cire tallafin mai. Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ne ya bada wan nan shawarar yayin taron manema labarai da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Wabba ya kara da cewa rashin darajar kudin Najeriya ne yake kawo wadan nan matsalolin inda yace matukar kudin Najeriya baya da mahimmancin ta fannin kasuwanci da kasashen waje haka ne zai cigaba da faruwa.

Shugaban na NLC ya kirayi gwamnati da tayi kokarin ganin ta habbaka matatun mai na kasar. Ya kuma kara da cewa dole ne a hada kai da Venezuela don acigaba da samun goyon baya daga ragowar kasashen Afrika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *