Njeriya: Sabon Gwamnan Jihar Borno Ya Ziyarci Gwoza

12042859_876148105789504_7732833326581756385_n
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil Ngala

jihar Borno dake arewa maso gabashin najeriya farfesa Babagana Umara Zulum ya fita ayyuka a wajen birnin Maiduguri a cikin yan kwanaki da aka rantsar dashi.

Farfesa Babagana ya fara da kauyen Limankara dake karamar hukumar Gwoza inda ya duba gadar da ta karye wadda ta hada jihohin Borno da Adamawa da kuma kasar Kamaru inda yaci alwashin sake gina hanya daga kauyukan Pulka zuwa Limankara.

Zulum yace gwamnatinsa zata samar da kayayyaki a makarantu, hanyoyin ruwa, da kuma bunkasa harhar noma a karamar hukumar da kuma hanyoyin tsaro ga manoma.

Mai kula da ayyukan jami’an sojoji a yanki Birgediya Janaral Abdulmalik Bulama Biu, yace hakan zai basu damar gudanar da ayyukan su da tafiya cikin sauki wanda yana daya daga cikin abubuwan dake kawo musu cikas wajen gudanar da ayyukansu.

Haka nan Gwamnan yayi alkawarin bada taimakon da ya dace ga Gwoza duk lokacin da ya yanke shawar komawa koda kafin sallah ne.

Sarkin Alh. Mohammad Shehu Idirisa Timta, ya bayyana godiyarsa ga gwamnan da ya fara zabar karamar hukumar Gwoza a matsayin inda ya fara ziyarta a wajen birnin Maiduguri inda ya kara da cewa mutanen Gwoza baza su taba dena gode masa ba da kumayi masa addu’a ya gama gwamnatin sa lafiya.

Haka nan sarkin yace kimanin kasha 80 na mutanen Gwoza manoma ne kuma indai an basu tsaro zasu iya kawo karshen yunwa a Najeriya.

Related stories

Leave a Reply