Nijeriya: Boko Haram Sun Kai Hari Kauye Kuda Dake Jihar Adamawa

By: Babagana Bukar Wakil Ngala

Maharan Boko Haram sun kai hari kauyen Kuda dake yankin Madagali a jihar Adamawa a Arewa maso gabashin Najeriya ranar Laraba inda daga bisani aka sake samun gawar mutum tara , a yanzu dai yawan mutanen da suka rasu a harin sun kai su 30.

An samu gawar ragowar 9 a cikin jejin dake kusa da kauyen inda ake zargin mutanen an kashe su ne yayin da suke nema gudu.

Wani mazaunin yankin mai suna Paul Waramulu ya shaidawa AFP ranar laraba cewa an bisu an kashe su ne yayin da sukayi yunkurin guduwa zuwa jejin.

Maharan sun kona kashi biyu daga cikin uku na garin kuma sun kwashe musu kayyayakin abinci.
Haka nan wani mai suna Simon Damina ya bayyana cewa bayan an duba cikin jeji yanzu gwawwakkin sun zama 30.

Kauyen Kuda na yankin Madagali dake jihar Adamawa, inda yake da nisan kilomita 285 daga arewacin babban birnin jihar wato Yola.

Har yanzu dai ba’a ji wani rahoto daga jami’an soji ko yansanda ba akan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *