
Shugaban kasar Nageria Muhammadu Buhari ya kaddamar da makarantar Mala Kachallah Memorial School mai dauke da gadaje 1220 a birnin Maiduguri dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Shugaba Buhari ya bayyana ilimi a matsayin kashin bayan ko wane cigaba yayin da yake bude makarantar.
Buhari wanda ya ziyarci jihar ziyarar kwana daya ya jagoranci bikin bude gurare da daman a ayyukan da gwamnan jihar Kashim Shettima ya samar.

Shugaban Muhammadu Buhari ya yabawa gwamnan kan ayyukan da ya samar musamman a bangaren ilimi wanda rikicin Boko Haram yayiwa babban rauni.
Shugaban ya kirayi iyaye dasu yi amfani da damar da suka samu sus aka yaransu a makarantun.
Yayin da ake zagawa dashi kwamishinan ilimi na jihar Musa Inuwa Kubo yace makarantar anyi tane ne don taimakawa marayu da kuma wadanda basu da karfi a yankunan.
Haka nan shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-amin Elkanemi ya godewa shugaban domin zuwansa gurin bude wadan nan ayyukan karkashin gwamnatin Shettima.
