
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMA da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki sun duba yadda za’a shawo kan wasu matsaloli a najeriya idan wasu masifu sun taso.
Darakta janaral na hukumar ta NEMA Alhaji Mustapha Maihaja ne ya bayyana hakan yayin rufe taron da suka shirya na kwana biyu kan wayar da kan jama’a akan tasowar wasu matsaloli a najeriya musamman saboda karatowar damuwa na shekarar 2019, wanda aka gudanar a Abuja.
Daraktan bincike da ceton jama’a na hukumar Air Commodore Akugbe Iyamu ne ya wakilci Maihajaa gurin taron inda yace hakan zai ceci ran mutane da dama idan suka kare kansu.

Ya kara da cewa faruwar abubuwan nada nasaba da yadda kasa ta shirya tarbar ko wace irin matsala idan ta fara ganin alamu, haka nan zasu saki duk wani muhimmin bayani kan abubuwan da zasu faru.
