Nigeria: MNJTF Sun Kashe Yan Boko Haram 39 A Kauyen Cross Kauwa Dake Jihar Borno

By; Babagana Bukar Wakil Ngla

Jami’an sojojin hadin gwiwa na Multi National Joint Task Force dake shiyya ta 2 a kasar Chadi dana shiyya ta 3 dake kasar Najeriya sun kashe yan kungiyar Boko Haram 39 yayin aikin da suke na OPERATION YANCIN TAFKI a kauyen Cross Kauwa dake kusa da tafkin Chadi.

Yayin harin, sojoji 20 sun samu raunuka inda aka mika su gurin da zasu karbar magani, haka nan sun samu makamai da dama.

Shugaban tsaron kasar Chadi Janaral Tahir Erda ya ziyarci sojojin a fagen dagar yayin da suke aikin karkashin Operation YANCIN TAFKI, inda ya samu tarba daga kwamnadan kasa Major General Olufemi Akinjobi a Kinnasara Cantonment dake Monguno.

General Erda ya kiraye jami’an dasu hada kansu don ganin an kawo karshen ta’addancin a yankin. Haka nan ya ziyarci asibitin da ake kula da sojojin da suka samu raunuka a fagen yakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *