Nigeria: Mayakan ISWAP Sun Kai Hari Kauyen Gajiganna Dake Jihar Borno

Fararen hula 2 da sojoji 3 ne suka rasa rayukansu yayin da aka kai hari arewa maso gabashin Najeriya ranar Asabar inji mazauna yankin da jami’an tsaro.

Yan bindigar da ake kyautata zaton mayakan ISWAP ne sun kai hari wani yanki na sojoji dake garin Gajiganna a jihar Borno.

Yan bindigar sun kashe sun kashe sojoji 2 da fararen hula kuma sunyi awon gaba da motar sojoji inji wani dan kungiyar sa kai Babakura Kolo. Haka nan sun kashe jami’an tsaron da fararen hula a kauyen Tungushe dake kusa dasu inji Kolo.

An kai harin Gajiganna da Tungushe bayan an kashe wasu jami’an tsaron Chadi guda 2 yayin da suka fafata da mayakan a arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *