Nigeria: Kwamitin Yan Gudun Hijira Na Majilisar Wakilai Sun Kai Ziyara Wasu Sansanonin A Jihar Borno

tmp_2722-reps1570630872
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamitin yan gudun hijira na yan majilisar wakilai wanda Hon. Enwo yake jagoranta ya kai ziyara wasu sansanin yan gudun hijira dake jihar jihar Borno ranar juma’a.

An dade dai ana fama da rikicin Boko Haram wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 27,000 san nan kimanin mutane miliyan 2 suka rasa matsugunansu a Arewa maso gabas.

Rikicin ya yadu har zuwa kasashen ketare irinsu Nijar, Chadi da Kamaru wanda hakan yasa suka hada jami’an tsaron hadin gwiwa don yaki da yan kungiyar.

Haka nan yan kungiyar ta Boko Haram sunyi garkuwa da dubban mata da yara a sassan kasar nan. yayin da yake jawabi Enwo ya bayyana cewa majalisar zata gudanar wani shiri mai suna ‘Kampala Convention’ don kawo karshen matsalolin da ake fama dasu a sansanonin.

Ya kara da cewa kwamitin zai hada kai da wasu kungiyoyin do a samu a maida yan gudun hijirar muhallansu.

Related stories

Leave a Reply