Nigeria: Hukumar Zana Jarabawar WAEC Ta Fitar Da Sakamakon Mutane 91, 225

WAEC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar zana jarabawar WAEC ta fidda sakamakon mutane 91, 225 wadanda suka rubuta jarabawar a makarantun sakandare.

Shugaban ofishin rubuta jarabawar Mr. Olu Adenipekun shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu inda ya ce cikin asu rubuta jarabawar 97,080 da suka yi rajista dubu 94,884 ne suka samu kyakkyawar sakamako.

Adenipekun ya ‘kara da cewa masu rubuta jarabawar sun samu kaso mafi rinjayi sa’annan ya ce za a sake fida raguwar sakamakon wadanda suka rubuta jarabawar anan gaba.

Hakazalika  ya cigaba da cewa an samu wasu daga cikin masu rubuta jarabawar 9,457 da laifin satar jarabawa wanda ya ce za su gurfana gaban ‘kwamitin zana jarabawar WAEC domin ladabtar da su.

Related stories

Leave a Reply