Nigeria: Hedikwatar Tsaro Ta Karyata Rahoton Da Wall Street Journal Ta Rubuta

Hedikwatar tsaro ta kasa ta karyata rahoton da Wall Street Journal ta rubuta kan cewa akwai inda ake binne jami’an soji da Boko Haram suka kashe a Arewa maso gabas ba tare da saninn iyalansu ba.

Hedikwatar ta bayyana wan nan zargin a matsayin mara tushe kuma wanda ya wallafa labarin bai san yadda jami’an soji suke martaba rayuwa da kuma yadda suke kula da wadanda suka rasa rayukansu ba.

Rahoton na dauke da sa hannun mataimakin Daraktan Hedikwatar ta hanyar yada labarai da kuma Col Onyema Nwachukwu.

Haka nan hedikwatar ta kirayi jam’an nata da jama’a da su yi watsi da wan nan zargin mara tushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *