
By: Babagana Bukar Wakil
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya wato EFCC ta kama dan kasuwar nan Babagana Abba Dalori, wanda ya damfari abokanan kasuwancinsa masu zuba jari kimanin Naira biliyan 7.
Dalori dan shekara 35, wanda ya gama karatunsa a fannin wutar lantarki a jami’ar Maiduguri cikin shekarar 2010, shine Manajan Darakta na kamfanin Galaxy Transportation and Construction Services Limited, inji hukumar ta EFCC.
Bincike ya tabbatar da Dalori ya samu kudinsa ta hanyar masu zuba jari wadanda yake yiwa dadin baki kan samun riba mai yawa yayin da suka zuba jarin, inda yake yiwa wasu alkawarin kashi 135 wasu ma har 200 na abin da suaka zuba.
Ata bakin wanda ake zargin ya bayyana cewa ya fara sana’ar a shekarar 2012 da babur mai kafa 3 wato Keke NAPEP, a shekarar 2014 ne daruruwan mutane suka nuna sha’awarsu suka shiga.
Ya kara da cewa a shekarar 2017 ya samu Naira miliyan 400, inda ya karbi takardar shaidar hakar ma’adanai a Mpape dake Abuja. Ya kuma bayyana cewa yana da ofisoshin a jihohi 11.
Bincike ya tabbatar da cewa mutane da suka zuba jari a kamfanonin dake da rijista a jihohi 3 Abuja, Maiduguri da Yobe basu samu komai ba.
Wasu da aka yi hira dasu sun bayyana cewa sun saka miliyan 2 zuwa miliyan 20, amma basa samu komai.
