Ndume ya gana da shugaba Buhari, kan tubbabun yan boko haram

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sanata Mohammed Ali Ndume, yayi tsayin daka wajen ganin cewa an hukunta duk wani dan boko haram din daya mika wuya.

sanatan mai wakiltar kudancin jihar borno, Ali Ndume ya bayyanawa haka bayya tattaunawa da shugaban kasa a fadar shugaban kasar a Abuja.

yace tsaffin yan ta’addan musamman wadanda keda jini a hanuun su, baza’a barsu haka kawai ba.

ya kara dacewa, dukda akwai marassa laifi acikin su, wadanda akayi amfani dasu amatsayin bayi da kauma kariya, dolea hukunta su bisa dokar kasa dakuma dokar kasa da kasa.

yace, dukda sun mika wuya, baza’a kashe su ba kamar yadda babu wanda zai sa abar su ba tareda hukunta su ba ta yadda doka ta tsara.

yace, biyo bayan hanyoyi da masu ruwa da tsaki na jihar borno suka tattauna, gwamnatin tarrayya zata kawo hanya mafi dacewa kan yadda za’a magance matsalar yan ta’addan dasuka tuba.

Leave a Reply