Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

NDLEA, Ta Yi Nasarar Cafke Wasu Kwayoyi Masu Dauke Da Hodar Iblis,

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

From Hamisu Ado Nguru.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta yi nasarar cafke wasu kwayoyi masu dauke da hodar iblis, heroin, methamphetamine da tabar wiwi da ake jigilar su zuwa kasashen Ingila, Northern Ireland, Australia, Maldives da New Zealand.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan hukumar, ta fannin yada labarai Femi Babafemi ya bayyana cewa an gano wani shahararren mai fataucin kwayoyin, Sikiru Owolabi, wanda ya bayanna akalla wasu guda biyu da aka kama.

Jami’an leken asirin da ke haɗe da kamfanonin jigilar kayayyaki na duniya guda biyu a ne ya bayyana kame kayan a jihar Legas.

Sikiru Owolabi ya bayyana bayani mai amfani cewa an samu kilogram 1 na hodar iblis da aka ɓoye a cikin kwantena mai wadda za’a kai Dublin dake Arewacin Ireland inda aka kam shi a jihar Legas.
Hakan yasa an gano wasu gram 200 na hodar iblis da za’a kai London, da kamfanin jigilar.

A wani aikin da aka yi a asirce, an kama gram 320 na kwayar heroin da aka boye a cikin ‘yan kunnen inda za’a kai kasar Kongo har zuwa Australia a wani kamfani daban da ke Lagas, kamar yadda aka kame wasu gram 390 da aka boye a cikin kayan maza kuma zuwa Arewacin Ireland duk da kamfanin .

Leave a Reply