NAOWA Zasu Horar Da Mata 400 A Birnin Maiduguri

Kungiyar matan sojojin Najeriya zasu kaddamar da ayyukan more rayuwa ga al’ummar birnin Maiduguri a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Sun bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar da ayyukan, shugabar kungiyar Aisha Bulama Biu ta bayyana cewa sunga ya dace ne a taimakawa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu yayin yaki da yan kungiyar Boko Haram.

Mrs Bulama tace ayyukan da suke yunkurin yi zasu taimakawa iyalan jami’an nasu da suka rasa rayukansu yayin rikicin na Boko Haram.

Ayyukan sun kushi samar da rijiyoyin burtsatsai, a kauyuka kamar su Auno, Shagari low cost housing estate B, Shuwari da waddiya.

Ta kara da cewa sun ga amfanin hakan ne soboda rashin ruwa da ake fama dashi a cikin Maiduguri don haka suka ga dacewar wan nan aikin.

Haka nan kunyoyar tasu zata koyawa mata 400 da suka rasa mazajensu sana’ar dogaro da kai. San nan sun shirya wasanni don a samu kyakkyawar ma’amala da mutane.

Uwar gidan mataimakin gwamnan jihar Hauwa Usman Mamman Durkwa ta yaba da wan nan kokarin na NAOWA a Maiduguri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *