Najeriya: Zulum Ya Ziyarci Gajiram Dake Karamar Hukumar Nganzai Bayan Harin Boko Haram

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana kokarinsa na ganin ya taimakawa jami’an tsaro wajen kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.

Zulums ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci Gajiram dake karamar hukumar Nganzai don yin ta’aziyya ga mutane bayan rasuwa yan garin fiye da 60 bayan da yan kungiyar Boko Haram suka kai musu hari.

Ya kara da cewa gwamnatinsa baza ta saurara ba har sai an samu tsaro a jihar gaba daya. San nan yayi alla wadai da harin inda ya kirayi mutane dasu dinga sa ido kuma su bawa jami’an tsaro hadin kai.

Haka nan yayi addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu da iyalansu kan Allah ya basu hakurin jure rashin da sukayi.

Gwamnan ya ziyarci babban asibitin birnin jihar don jajantawa wadanda suka samu raunuka yayin harin.

Related stories

Leave a Reply