Najeriya: Zulum Ya Amince Da Biyan Kudaden Ma’aikatan Da Sukayi Ritaya 1000

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno farfesa BabaganaUmara Zulum ya amince da biyan kudaden ma’akatan gwamnati da sukayi ritaya daga shekarar 2013 zuwa yanzu karo na biyu su 1000.

Wan nan yazo bayan da gwamnan ya biya kasha na farko na mutane 1,684 na masu ritayar a wata 2 da suka wuce.

Babban mai bada shawara na musamman kan hulda da jama’a Malam Isa Gusau ne ya bayyana hakan a madadain gwamnan inda yace tuni aka aika kudaden bankunan da zasu biya kudaden da masu ritayar suka bayar.

Gusau ya kara da cewa za’a fitar da sunayen wadanda aka biya din a yau, kuma duk wanda bai ga kudin nasa ba a cikin sunaye sai ya rubuta takardar korafi ta hanyar kungiyar yan fansho din sai ta mika ofishin shugaban ma’aikatan don biyan nasu kudaden.

San nan ya bayyana cewa ya lura cewa a jihar Borno ana biyan yan fansho hakkokinsuakan kari a shekaru 8 da suka gabata.

Haka nan ya kara da cewa a watan Augusta na wan nan shekarar Zulum, ya amince da biyan ragowar kudaden ma’aikata 9,898 na jihar da biyan kudaden wadanda suka rasu su 185 ga iyalansu.

Related stories

Leave a Reply